'Abdul Samad Rabiu ne mutum na biyu mafi arziki a Najeriya'
Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya zarce fitaccen attajirin nan Mike Adenuga, inda ya zama mutum na biyu mafi arziki a Najeriya.
Mujallar Forbes mai wallafa mutanen da suka fi arziki a duniya, ta ƙiyasta arzikin shugaban kamfanin na BUA, da kimanin dala biliyan 7.2, lamarin da ya sa ya zama na biyu mafi arziki a Najeriya, na huɗu a nahiyar Afirka, wanda kuma ke matsayi na 249 a duniya.
Ana alaƙanta ƙaruwar arzikin attajirin da bunƙasar darajar kamfaninsa wanda ke samar da abinci.
Hannayen jarin kamfanin BUA sun samu bunƙasa da kusan kashi 10 cikin 100, a farkon watan Janairun 2024, lamarin da ya sa jarinsa ya ƙaru da dala biliyan 1.92.
A yanzu AbdusSamad Rabi'u, mai shekara 63, ya zarta Mike Adenuga wanda a yanzu ƙarfin jarinsa yake dala biliyan 6.6.
Mike Adenuga - mai kamfanin Globacom - ya samu raguwar arziki da dala miliyan 400, kamar yadda mujallar Forbes ɗin ta nuna, wanda kuma ya koma matasayi na uku a Najeriya na shida a Afirka, sannan yana mataki na 418 a duniya.
Sai dai har yanzu Aliko Dangote ne ke kan gaba a matsayin wanda ya fi kowa arziki a Najeriya da Afirka.
0 Comments