Gida Najeriya: Gamnatin jihar Legas ta haramta amfani da robar sayar da abinci

 Gamnatin jihar Legas ta haramta amfani da robar sayar da abinci



Gwamnatin jihar Lagos ta ce nan take za ta fara aiwatar da dokar da ta hana amfani da robar da masu sayar da abinci ke amfani da ita da kuma wasu robobi.


Kwamishinan muhali na jihar, Tokunbo Wahab ya ce robobi na taka muhimiyar rawa wajen gurɓata muhali saboda sai an ƙonasu ake iya kawar da su.


Jami'an gwamnatin jihar ta Lagos sun ce dokar da aka zartar a 2009 ta nemi a hukunta ko ci tarar duk wani da aka samu da laifi.


Kwararru a duniya sun yi ƙiyasin cewa Najeriya na samar da tan miliyan biyar na sharar robobi a kowace shekara.

Post a Comment

0 Comments