Gwamnan Jigawa Ya Kaddamar Da Shirin Farfado Da Ilimi Ta Amfani Da Fasahar Zamani "JIGAWACOMPETE"
Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa Mallam Umar Namadi FCA, ya kaddamar da shiri mai suna Jigawa Compete (JCompete), wato wani shiri mai wanda aka kafa da nufin farfado da ilimi a jihar Jigawa.
Matakin farko na wannan shiri ya mayar da hankali ne kan Karfafa Ilimi ta hanyar rarraba manyan wayoyon hannu guda 300, da samar da hanyar sadarwa ta Intanet, da aiwatar da tsarin samar da ilimi ta amfani da fasahohin zamani (EMIS).
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a babban dakin taro na Sir Ahmadu Bello, dake sakatariyar jiha. Sannan Shirin ya kasance wani muhimmin al'amari a yunkurin jihar Jigawa na shigar da fasahar sadarwa ta zamani cikin harkokin ilimi domin bunkasa fannin.
A kashi na farko na Shirin bunkasa ilimi na JigawaCompete an raba manyan wayoyin hannu guda 300 ga shugabanni makarantu da jami’an kula da ilimi na shiyya, don tabbatar da cewa sun samu damar yin amfani da fasahar zamani a fannin koyo da koyarwa. Har ila yau shirin ya haɗa da samar da ingantaccen Intanet, don tabbatar da cewa ɗalibai za su iya amfani da shafin yanar gizo akodayaushe suke da bukatar fadada iliminsu, da sauran bukatunsu na ilimi.
Gwamna Namadi ya jaddada cewa shirin JigawaCompete mataki ne na shirya matasa domin su samu kwarewa da cigaban da ake bukata ta hanyar fasahohin zamani. Ta hanyar shigar da fasahar sadarwa ta zamani cikin ilimi, jihar Jigawa za ta Kai ga bunkasa kirkire-kirkire, da inganta sakamakon koyo da koyarwa, da kuma baiwa dalibai dabarun da suka dace don samun nasara a karni na 21.
Muhammad Isma'el
SA Publication and Photography.
0 Comments