Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi Ya Kaddamar Da Tubalin Kafa Harsashin Aikin Gina Gidaje 1500 A Fadin Jihar Jigawa.

Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi Ya Kaddamar Da Tubalin Kafa Harsashin Aikin Gina Gidaje 1500 A Fadin Jihar Jigawa. 



Babban Bako Na Musamman Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Kana Kuma Babban Ministan Tsaro Na Nigeria H.E Muhammad Badaru Abubakar MNI, MON Wadda Ya Kafa Harsashin Ginin A Fanisau Dake Dutse Inda Gwamnatin Jihar Jigawa Zata Gina Gidaje 600 A Babban Birnin Na Dutse,


Haka Zalika Sauran Ragowar Gidajen Zasu Kasance A Kananan Hukumomin Hadejia, Ringim, Kafin Hausa, Kazaure, Birnin Kudu, Gumel Dakuma Babura, 


Babban Ministan Tsaro Alhaji Muhammad Badaru Abubakar MNI, MON, Cikin Jawabinsa Ya Yabawa Magajin Nasa Gwamna Mallam Umar Namadi FCA Bisa Kokarin Dayake Domin Ganin Jihar Jigawa Ta Bunakasa Tareda Dumbum Al’ummar Jihar Jigawa Wadda Kema Jihar Addu’o’i Na Musamman 


Haka Kuma Babban Ministan Na Tsaro Ya Shaidawa Gwamna Namadi Tareda Sauran Mahalarta Taron Cewa Jihar Jigawa Ta Kasance Ta Daya A Bangaren Zaman Lafiya A Jadawalin Wannan Sabuwar Shekarar Na 2024 Inda Ya Kara Kira Ga Al’ummar Jihar Jigawa Wajen Cigaba Da Yiwa Shugabanni Addu’a Tareda Basu Shawarwari Na Musamman, 


Gwamna Namadi Yayin Jawabinsa Ya Kara Tabbatar Kokarin Da Gwamnatinsa Take A Bangarori Da Dama Domin Ganin Jihar Jigawa Ta Fara Gogayya Da Sauran Jihohi Ta Fuskoki Daban Daban,


Taron Wadda Yasamu Halartar Katafanin Mukarraban Gwamnatin Jihar Jigawa, Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Jigawa Hon. Aminu Sani Gumel, Mai Martaba Sarkin Dutse HRH Hameem Muhammad Sunusi Tareda Shugaban Sojojin Nigeria. 


Muhammad Isma'el 

SA Publication and Photography.

Post a Comment

0 Comments