Gwamnan Jihar Katsina, Mal. Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da shirin daukar nauyin ɗalibai arba'in da daya 41 zuwa kasar Egypt karatu.

Gwamnan Jihar Katsina, Mal. Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da shirin daukar nauyin ɗalibai arba'in da daya 41 zuwa kasar Egypt karatu.



Gwamnan Jihar Katsina, Mal. Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da shirin daukar nauyin ɗalibai arba'in da daya 41 da Gwamnatin Jihar Katsina ta daukin nauyin karatunsu zuwa ƙasar Egypt, a birnin Cairo da za su yi digiri na farko akan likitanci.


An kaddamar da shirin a ɗakin taro na masaukin shugaban ƙasa a gidan Gwamnatin Jihar Katsina da sanyin safiyar Litinin din nan.


Shugaban kwamitin, mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon. Faruk Lawal Jobe ya yi jawabi akan irin ƙoƙarin da Gwamnatin Gwamna Mal. Dikko Radda ta yi na ware maƙuddan kudade da za ta ɗauki nauyin karatun ɗaliban da aka zaɓo daga ƙananan hukumomin talatin da hudu na Jihar Katsina da za su amfana da tallafin karatun zuwa ƙasar Egypt da za su yi karatun likitanci da sauran ɓangarorin kiwon lafiya. Shugaban kwamitin ya ƙara da cewa Gwamnati za ta ba da ƙuɗi Dala ɗari biyu ga kowane ɗalibi kafin tafiyar.


Hon Faruk Lawal Jobe ya bayyana wasu daga nasarorin da kwamitin ya samu a yayin tantance ɗaliban da za su amfana musamman wadanda suka yi karatu a makarantu Gwamnati kuma suke da makin da ake buƙata kafin samun damar amfana da tallafin karatun.


Mal. Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa Gwamnati jiha ta zaɓo ɗaliban domin ba su tallafin karatun zuwa ƙasashe a ƙoƙarin na inganta sha'anin kiwon lafiya tare da taimaka wa matasan Jihar Katsina, Mal. Dikko Umaru Radda ya ƙara cewa ya kamata ɗaliban da suka amfana da tallafin zuwa karatun su sani cewa Gwamnati ta ɗauki kuɗaɗen al'ummar Jihar Katsina ta ƙashe da manufar cewa za su zama jakadu nagari da za su fidda Jihar Katsina kunya.


Hakazali Mal. Dikko Umaru Radda ya jaddada cewa yadda kwamitin da Gwamnati ta naɗa ya gudanar da aikin shi wajen ganin ya zaɓo mutanen da suka cancanta ba tare da alfamar ba Gwamnati za ta cigaba da ƙoƙari wajen bibiyar karatunsu a makarantun da za'a kainsu kuma duk wanda aka samu da rashin maida hankali Gwamnati zata maye gurbinshi da wani.

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Radda.


Ku kasance da muryar Labarai domin samun ingantattun labaranmu.

Gaskiya Tsantsarta.

Post a Comment

0 Comments