Gwamnatin jihar Katsina ta amince da ware hili hekta 25 ga Gwamnatin Tarayya domin gina gidajen ‘Renowned Hope City’ a Jihar Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta amince da ware hili hekta 25 ga Gwamnatin Tarayya domin gina gidajen ‘Renowned Hope City’ a Jihar Katsina 



Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Dakta Dikko Umaru Radda, ta amince da baiwa gwamnatin tarayya fili mai girman hekta 25 domin gina Renewed Hope City Project a jihar.


An isar da wannan amincewa ga mai girma ministan gidaje da raya birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ta hannun Honorabul kwamishinan filaye da safiyo na jihar Katsina, Dr Faisal Kaita, a hedikwatar ma’aikatar dake Abuja.


A watan Oktoban shekarar da ta gabata, gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin gina sabbin garuruwa a fadin kasar nan, tare da gina gidaje kusan 1000 a kowace jiha da kuma gidaje kusan 4,000 a babban birnin tarayya Abuja. Wannan yunƙuri na nufin samar da gidaje masu rahusa ga ƴan Najeriya daidai da sabon tsarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, akan Gidaje da Raya Birane.


Gwamnatin jahar Katsina itace ta farko a jahohin Nigeria da fara amincewa da bada filin.

Post a Comment

0 Comments