Gwamnatin tarayya ta soke lasisin shaidar digiri daga Jamhuriyar Benin da Togo.

 Gwamnatin tarayya ta soke lasisin shaidar digiri daga Jamhuriyar Benin da Togo.



Hakan ya faru ne biyo bayan rahoton sirri da jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Akan yacce ake samun digiri cikin gaggawa ba tare da cancanta ba.


A cikin rahoton da aka buga a ranar 30 ga watan Disamba na shekarar Dubu biyu da ashirin da ukwu. Daily Nigerian ta fallasa yadda jami'an Gwamnati masu cin hanci da rashawa ke taimakawa Sana'ar damfarar takardar sheda.


Rahoton ya fallasa yacce wakilin jaridar Daily Nigerian Umar Audu ya kammala shirin digiri na tsawon shekara hudu a kasa da watanni biyu daga Ecole Superieure de Gestion.


Umar Audu yayi magana da Jami'in da yakeda ruwa da tsaki a bangaren samun sakamakon kammala karatun inda ya nemeshi Akan Yana bukatar a samar mashi da shaidar kammala karatun digiri Jami'in yace dashi "wannan Abu ne Mai sauki ya fada mashi Yan kudaden da zai bayar" Hakan kuwa akai bayan ya bashi cikin kasa da sati shidda saiga shaidar kammala digiri da sakamako mafi girma.


Umar Abdu ya haye dukkan wasu bincike da akeyi don zuwa bautar kasa batare da Jami'in Dake bincike sun gano cewa wannan shaidar ta bogi bace ba.


Zuwa yanzu dai jaridar Daily Nigerian tayi nasara Akan binciken kwakwaf din da tayi inda aka soke lasisin wannan digiri Dan Cotonou.

Post a Comment

0 Comments