Gwamnonin Jam'iyyar APC, Sun Gana Da Shugaban Kasa Tinubu

 Gwamnonin Jam'iyyar APC, Sun Gana Da Shugaban Kasa Tinubu.



A yau Juma'a 12 ga watan Junairun shekarar 2024, Gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi FCA ya gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a ziyarar da kungiyar Gwamnonin jam'iyyar APC ta kai masa, a Abuja. 


Kungiyar Gwamnonin ta gana da shugaban kasa domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ciyar da kasar Nan gaba.


Idan ba'a manta ba a ranar Laraba 10 ga watan da muke ciki, Kungiyar Gwamnonin Jam'iyyar APC ta gudanar da taro a gidan Gwamnatin jihar Imo, inda suka cimma matsaya kan marawa dukkan manufofi da tsare tsaren gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.


Muhammad Isma'el 

SA Publication and Photography.

Post a Comment

0 Comments