Halin da ake ciki Akan Hare-haren da ke faruwa a kasashen Falasdinu, Iraki, Siriya, Iran, Pakistan da kuma Lebanon.

Halin da ake ciki Akan Hare-haren da ke faruwa a kasashen Falasdinu, Iraki, Siriya, Iran, Pakistan da kuma Lebanon.  




Hare-haren da ke faruwa a kasashen Falasdinu, Iraki, Siriya, Iran, Pakistan da kuma Lebanon 


Haramtacciyar kasa Isra'ila na kisan kiyashin Falasdinawa a Gaza fiye da kwanaki 100, a lokaci guda kuma suna musayar wuta da Hizb*** da ke samun goyon bayan jamhuriyyar Musulunci ta Iran a Lebanon.


Ƙungiyoyin gwagwarmaya wadanda suke samun goyon bayan Iran a Iraki da Siriya suna farmakar sojojin Amurka a Siriya da Iraki, sun ma tarwatsa sansanonin sojojin Amurka da yawa a Iraki, tare da tarwatsa wuraren leken asirin Haramtacciyar kasar Isra'ila. Ita kuma Amurka da Birtaniya suna kai hare-hare kan Yemen da ke samun goyon bayan Iran. Bayan da 'yan gwagwarmayar Yemen suka datse kogin maliya suna tarwatsa jiragen haramtacciyar kasar Isra'ila tare da hana su wucewa ta kogin lamarin da ke yi wa tattalin arzikin yammaci barazana.  


Makonni kadan da suka gabata, kungiyar 'yan ta'addan Da'esh da suka fito daga Pakistan ta kai tagwayen hare-haren bama-bamai a Kerman dake Iran inda ta kashe mutum fiye da 100 da raunata mutum fiye da 200.  


Wannan ya sanya Iran ta maida da martani da makaman mizayil a birnin Saravan dake iyaka da Pakistan kan 'yan ta'addan da suka fito daga Pakistan inda ta kashe gommai. Wannan harin ramuwar gayyar na Iran kan 'yan ta'addan Da'esh ya fusata Pakistan, inda suka datse huldar diflomasiyya da Iran. 


A yau Alhamis Pakistan ta kai hari a wani kauye a Iran dake iyaka da Pakistan din, lamarin da ya sanya mutum bakwai suka rasa ransu; mata uku da yara kanana hudu. Iran ta ce dukkanin mutum bakwai din da Pakistan ta kashe, babu Ba'iraniye ko guda daya.

© Ammar Muhammad Rajab

Post a Comment

0 Comments