Hamas ta nemi ICRC ta dauki mataki kan dokokin da Isra'ila ta karya na kare 'yancin Falasdinawa fursunoni.
Kungiyar Hamas da ke fafutukar kare mutuncin Falasdinawa ta yi kira ga kungiyar agaji ta International Committee of the Red Cross [ICRC] da ta tattara irin dokokin kara hakkin dan'adam na Falasdinawan da ke tsare a gidajen yari da Isra'ila ta karya, musamman yadda take gallaza wa mata.
A wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta bukaci ICRC da sauran kungiyoyin kare hakkin dan'adam "su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na daukar mataki kan cin zali da take 'yanci da Isra'ila ke yi wa mata Falasdinawa wadanda ke tsare a gidajen yarinta."
Sanarwar ta kara da cewsa "Matan Falasdinawa da ke tsare a gidajen yari suna fuskantar tsananin rashin abinci da hana su magunguna."
Alkaluman baya bayan nan sun nuna cewa Falasdinawa sama da 7,800 ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila, ciki har da mata 80.
0 Comments