Har yanxu yakin Sudan ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin dakarun sojin kasar da dakarun RSF

 Har yanxu yakin Sudan ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin dakarun sojin kasar da dakarun RSF.



Makomar Sudan ta fada cikin rashin tabbas tun bayan barkewar rikici tsakanin dakarun sojin kasar da dakarun RSF na tsawon watanni tara da suka gabata.

Irin mugun yakin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da kuma rudunar RSF tun daga Afrilun 2023 ya ci gaba har cikin sabuwar shekarar 2024, inda Sudan din ta yi wa jakadanta da ke Kenya kiranye sakamakon abin da ta kira karbar da kasar ta yi wa abokin adawarsu Mohamed Hamdan Dagalo babban kwamandan RSF.


Duk da cewa Kenya ta yi karin haske kan cewa tattaunawar da aka yi tsakanin Shugaba William Ruto da Dagalo a ranar 3 ga watan Janairu an yi ta ne domin kara tabbatar da zaman lafiya a Sudan, sai dai gwamnatin mulkin Sudan din na kallon lamarin a matsayin cin mutunci.


Wannan matsalar ta diflomasiyya ta faru ne tun bayan Dagalo ya soma wani shiri na zuwa kasashe bayan sama da mutum 12,000 suka rasu inda aka raunata sama da mutum 33,000. Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum miliyan 6.6 sun rasa muhallansu.


Shekarar bakin ciki


A farkon 2023, 'yan Sudan ba su san cewa kasarsu za ta fada cikin yaki bayan wata hudu da shiga sabuwar shekarar ba.


Sai dai abin mamakin, jam'iyyu biyun da suka yi aiki tare domin hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir su ne suka rinka yaki da juna.

Yakin da ya barke tsakanin RSF da sojojin Sudan ya kawar da duk wata fata da ake da ita na zabar sabuwar gwamnati a shekara biyu, karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa a 2022 tsakanin sojojin kasar da kuma jam'iyyu.


Tun daga lokacin, an ta samun bala'o'i a Sudan, wadda ita ce kasa ta uku mafi girma a Afirka mai mutum miliyan 48.


Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa jama'ar kasar na matukar bukatar taimako sakamakon wannan yakin.


Zuwa Disambar 2023, sama da mutum miliyan 6.6 suka rasa muhallansua ciki da wajen kasar. Sai da kasashen Chadi da Masar da Sudan ta Kudu masu makwaftaka suka rinka bayar da taimako ga 'yan Sudan din da ke guduwa saboda yakin.


Duka janarorin biyu masu rikici da juna ba su tabuka wani abin a zo a gani ba da zai iya kawo karshen wannan yakin, duk da lamarin yana kara tabarbarewa a kullum. Kokarin da aka rinka yi na shiga tsakanin bangarorin biyu bai haifar da wata mafita ba.


"Da sojojin Sudan din da RSF din na takama da karfi inda duka suke ganin kamar za su iya magance matsalolinsiu ta hanyar yaki," in ji Dakta Edward Githua, wanda kwararre ne ta bangaren harkokin kasashen waje a tattaunawarsa da jaridar TRT Afrika.

Kusan mutum miliyan 17.7 a fadin Sudan, wanda adadin ya kai kaso 37 a cikin 100 ke fuskantar karancin abinci tsakanin Oktobar 2023 zuwa Fabrairun 2023," kamar yadda wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta FAO ta bayyana a wani sabon rahoto.


"Akasarin jama'ar da ke fama da tsananin karancin abinci na zaune ne a jihohin da yakin ya shafa, daga ciki har da Darfur da Greater Kordofan da Khartoum - da Bahri da Omdurman.


Rahoton na FAO ya kuma ruwaito cewa ana ta aikata sace-sace a kasuwanni da bankuna da masana'antu da kuma gine-ginen gwamnati.

Post a Comment

0 Comments