Hukumar EFCC ta kama tsohon minista, Charles Ugwuh, bisa zargin almundahanar naira biliyan talatin da shidda.

Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta shiyyar legas  sun cafke tsohon ministan kasuwanci da masana’antu, Charles Chukwuemeka Ugwuh, bisa zarginsa da hada baki da kuma zamba har naira biliyan talatin da shidda.

An kama Ugwuh ne tare da Cif Geoffrey Ekenma a ranar 11 ga Janairu, 2024, a No.2, Musa Yar Adua Way, New Owerri, Jihar Imo, bayan wata takardar koke ga Hukumar daga wani ma'aikacin  banki, Ebony. 

Bincike ya nuna cewa Ugwuh da Ekenma, Manajan Darakta na Ebony Agro Industries Ltd., ana zargin sun samu bashi daga bankin domin saye da samar da shinkafa. 

Sai dai wanda ake zargin, a cewar mai shigar da kara, ya kasa cika hakkinsa na bankin, kuma duk kokarin da ya yi na ganin ya biya bashin kudin ya ci tura. Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

Post a Comment

0 Comments