Hukumar Hisbah ta Kano ta kama babbar mota dauke da kwalaben giya 24,000.

 Hukumar Hisbah ta Kano ta kama babbar mota dauke da kwalaben giya 24,000.



Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wata babbar mota makare da kwalabe daban-daban na barasa fiye da 24,000 da aka kwace daga hannun masu fasa kwauri a tsakar dare. 


Babban Daraktan hukumar, Alhaji Abba Sufi, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a hedikwatar hukumar yayin da yake duba motar da aka kwace daga hannun masu fasa kwauri a hanyar Zariya a daren ranar Talata. 


"Motar dake dauke da kwalabe daban-daban na barasa sama da 24,000 an kwace daga hannun masu fasa kwauri a hanyar Zaria a tsakar dare," in ji Sufi. 


Ya kara da cewa jami’an Hisbah a jihar sun zage damtse wajen aiwatar da dokar hana fasa kwaurin barasa da sauran abubuwa masu sa maye a jihar ta kan iyakokin jihohinta da ke makwabtaka da ita.

Post a Comment

0 Comments