Iran ta ce ta kai hari kan 'hedikwatar Mossad' ta Isra'ila a Iraki da Syria.
Sojojin juyin juya hali na Iran sun ce sun harba makami mai linzami hedikwatar leken asirin Isra'ila a Iraki da Syria, haka kuma sun kai hari kan 'yan ta'addan Daesh.
Sojojin juyin juya halin Iran sun ce sun kai hari da makami mai linzami kan hedikwatar ofishin leken asirin Isra’ila na Mossad da ke Iraki da Syria, kamar yadda kafofin watsa labarai suka ruwaito.
“Rundunar Juyin Juya Hali ta Musulunci ta sanar da lalata hedikwatar leken asiri da tattara bayanai na kin jinin Iran [Mossad] a sassan yankunan da makamai masu linzami,” kamar yadda kafar watsa labarai ta IRNA ta ruwaito a ranar Talata.
“Wannan hedikwatar ta kasance wata cibiya ta leken asiri da kuma shirya hare-haren ta’addanci a yankin,” in ji ta. Kafar watsa labarai ta Fars ta ruwaito cewa an lalata hedikwatar Mossad ta Isra’ila a yankin Kurdawa na Iraki.
Sannan kuma an kashe farar hula akalla hudu da kuma raunata shida a wani hari da aka kai a Erbil, kamar yadda Majalisar Tsaro ta Gwamnatin Yankin Kurdawa ta bayyana a wata sanarwa inda ta bayyana harin a matsayin “laifi”.
Haka kuma sojojin juyin juya halin sun kaddamar da harin makami mai linzami kan wuraren “’yan ta’adda” da ke Syria domin mayar da martani kan tagwayen bama-bamai na kunar bakin wake da aka yi a Iran a wata nan wadanda kungiyar ta'addanci ta Daesh ta dauki nauyin kaiwa, kamar yadda kafar watsa labarai ta kasar ta ruwaito.
0 Comments