Isra'ila ta kai hari a ofishin kungiyar Palestinian Red Crescent.

 Isra'ila ta kai hari a ofishin kungiyar Palestinian Red Crescent.



Jiragen yakin Isra'ila sun kai hari a ginin kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent Society (PRCS) inda suka kashe mutum guda tare da jikkata mutum shida.


Kungiyar ta wallafa bidiyo da ya nuna cewa harin ya sauka a gininta da ke birnin Khan Younis.


Kungiyar ta PRCS, wadda ke bayar da agajin magunguna da na jinkai, ta fuskanci hare-hare a yakin da Isra'ila ta kaddamar a Gaza.


Kazalika Isra'ila ta kashe Falasdinawa 14, ciki har da kananan yara tara, a jerin hare-haren da ta kai a yammacin birnin Khan Younis na Gaza, a cewar ma'aikatar kiwon lafiya ta yankin.


Isra'ila ta jefa bama-bamai masu nauyin tan 65,000 a 'yakin kare-dangi' na Gaza


Sojojin Isra'ila sun yi harba makamai masu linzami fiye da 45,000 da luguden bama-ba masu nauyin sama da tan 65,000 tonnes a yakin da take yi a Gaza, a cewar Ofishin Watsa Labarai na Gwamnatin Gaza.


"Jiragen yakin sojoji mamaya sun harba makamai masu linzami fiye da 45,000 da manyan bama-bamai, wasu daga cikinsu na da nauyin tan dubu biyu, a hare-haren kare-dangi na yakin da suka yi a Zirin Gaza, kuma da gangan suke kai hari kan gidaje," in ji ofishin.


"Nauyin bama-baman da sojojin suka harba a Zirin Gaza ya zarta tan 65,000, wanda ya fi nauyin bama-baman nukiliya guda uku da aka jefa a birnin Hiroshima na kasar Japan."


Ofishin ya ce kusan kashi "biyu cikin uku na bama-bamai da makamai masu linzamin...ana harba su ne a ko'ina ba tare da kiyaye kowanne wuri ba."

Post a Comment

0 Comments