Isra'ila za ta kare kanta a gaban kotun duniya kan zargin kisan ƙare dangi a Gaza.
Isra'ila za ta bayyana a gaban kotun duniya don kare kanta kan zargin da Afrka ta Kudu ta yi mata na aikata "kisan ƙare dangi" a Gaza, a cewar kakakin gwamnatin Isra'ila.
A ranar Juma'a ne Afrika ta Kudun ta shigar da ƙara a gaban kotun, wadda ita ce babbar kotun duniya.
Fadar gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce ya zama dole ga ƙasar ta kare aukuwar "kisan ƙare dangi".
Da yake mayar da martani, kakakin Isra'la, Eylon Levy ya bayyanawa taron manema labarai a ranar Talata cewa: "ƙasar Isra'ila za ta bayyana a gaban kotun duniya da ke Hague don wanke kanta daga ɓata sunan da Afrika ta Kudu ta yi mata na zubar da jini, wanda hankali ba zai ɗauka ba.
"Muna tabbatar wa shugabannin Afrika ta Kudu cewa, za su ga sakayya abin da suka aikata."
Afrika ta Kudu tana kakkausar suka ga matakan sojin da Isra'ila ke dauka a Gaza a tsawon yakin da ta kaddamar.
Harin da Hamas ta kai kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba ne ya haifar da yakin da ake yi a halin yanzu tsakanin bangarorin biyu.
Hamas ta kashe kimanin mutane 1,200 mafiya yawansu fararen hula.
Kuma kungiyar ta yi garkuwa da wasu mutane 240.
Yayin da fiye da mutane 22,000 mafiya yawansu kananan yara da mata aka kashe a Gaza a hare-haren da Isra'ila ke kai wa, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas.
0 Comments