Iyalan Wadanda Aka Sace a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Sun Roki ‘Yan Nijeriya Da Su Taimaka Musu da Naira Miliyan 50 Domin Biyan Kudin Fansar ‘Yan Uwansu

 Iyalan Wadanda Aka Sace a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Sun Roki ‘Yan Nijeriya Da Su Taimaka Musu da Naira Miliyan 50 Domin Biyan Kudin Fansar ‘Yan Uwansu.




Rahotanni sun bayyana cewa iyalan matafiya daga Kaduna zuwa Abuja da aka sace suna neman kudade daga al’ummar Najeriya domin biyan Naira miliyan 50 da ‘yan ta’addan suka nema a matsayin kudin fansa.


Akalla mutane 85 ne da suka hada da Mata da Maza matafiya da rahotanni suka bayyana wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su a Katari da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, cikin karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna a tsakanin ranakun 6 zuwa 7 ga watan Janairu.


'Yan bindigar kuma sun kashe mutane hudu.


Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya bayyana cewa an yi artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga da suka yi yunkurin tare hanyar Kaduna zuwa Abuja a unguwar Dogon Fili zuwa Jere a ranar 6 ga watan Janairu, inda wasu daga cikin ‘Yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga.


Ya bayyana cewa, a yayin da ake fafatawa da ‘yan bindigar, mutane shida da ke kan hanyar sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.


Amma ‘yan sandan sun musanta cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane.


Sai dai a wani sako ta kafar sadarwar WhatsApp, iyalan wadanda aka sace sun bayyana cewa wadanda ‘yan ta’addan suka sace sun hada da ‘ya’ya 9 daga iyalan Alhaji Ibrahim Sadoh da kuma Alhaji Abdulwahab Abubakar, inji rahoton PUNCH.

Post a Comment

0 Comments