Jirgin yakin Nijar ya kashe fararen-hula 'bisa kuskure'


Jirgin yakin Nijar ya kashe fararen-hula 'bisa kuskure'

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne bayan jami'an tsaro sun hango wasu 'yan bindiga a kan babura suna tsara yadda za su kai hare-hare a yankin Libiri Bulangiga da Garbunwa ranar Juma'a da daddare zuwa safiyar Asabar.

Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya ce an samu kyautatuwar tsaro a kasar tun bayan da suka karbi mulki a watan Yulin da ya gabata.


Ma'aikatar Tsaro ta Jamhuriyar Nijar ta ce wani jirgin yakin rundunar sojin saman kasar ya kashe fararen-hula bisa kuskure a harin da ya kai wa 'yan ta'adda a jihar Tillaberi da ke kan iyaka da Burkina Faso.


Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da aka karanto a gidan talbijin na kasar RTN ranar Asabar da maraice.


Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne bayan jami'an tsaro sun hango wani gungun 'yan bindiga a kan babura yana tsara yadda zai kai hare-hare a yankin Libiri Bulangiga da Garbunwa ranar Juma'a da daddare zuwa Asabar da safe.


Daga nan ne aka bai wa jirgin yaki umarnin kai musu hari kuma an yi nasarar kashe 'yan bindigar.


Sanarwar ta kara da cewa washegari da jami'an tsaro suka je yankin da lamarin ya faru don duba halin da ake ciki sun gano cewa jirgin yakin ya kashe fararen-hula, ko da yake ba ta fadi adadin wadanda suka mutu ba.


Ma'aikatar Tsaron ta ce an kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin ba su kulawa.


Jirgin yaki ya yi hatsari


A wata sanarwa ta daban, Ma'aikatar Tsaron Nijar ta ce wani jirgin yakin rundunar sojin saman kasar ya yi hatsari a kan iyaka da Burkina Faso.


Sanarwar ta ce jirgin ya fadi ne ranar Juma'a da misalin karfe 12:15 na rana.


"Jirgin rundunar sojojin saman Nijar ya yi hatsari ne a yayin da yake kokarin sauka a wani sansanin sojoji da ke garin Kantchare kusa da iyaka da kasar Burkina Faso," in ji sanarwar.


Sai dai sanarwar ta ce babu wanda ya rasu ko da yake jirgin ya lalace sannan jami'i daya da ke cikinsa ya samu rauni, wanda nan-take aka yi masa magani.

Post a Comment

0 Comments