Kasar Saudiyya ta gano tarin tarin zinare a yankin Makkah.

 Kasar Saudiyya ta gano tarin tarin zinare a yankin Makkah.



A baya-bayan nan ne Saudiyya ta sanar da gano wani ‘gagarumin albarkatun zinare’ a cikin Masarautar.

 Kamar yadda sanarwar ta bayyana, an gano albarkatun zinare masu yawa a wani tazarar kilomita 100 kudu da wurin hakar gwal na Mansourah Massarah da ke gundumar Al Khurmah, a yankin Makkah. 

Kamfanin hakar ma'adinai na Saudi Arabiya (Maaden) ya bayyana cewa, an gano tarin zinare da dama, wanda ke nuni da yuwuwar fadada hakar zinare a yankin. 

Wannan binciken ya nuna sakamakon farko na babban shirin binciken Maaden wanda aka ƙaddamar a cikin 2022, da nufin kafa layin samar da ƙarfe.

Post a Comment

0 Comments