Kotu ta tasa keyar Danbilki Kwamanda zuwa gidan Dan kande bisa kalaman tunzuri

Kotu ta tasa keyar Danbilki Kwamanda zuwa gidan Dan kande bisa kalaman tunzuri.



Wata kotun Majistarea jihar Kano ta aike da Abdulmajid Ɗan bilki Kwamanda zuwa gidan yari bisa zargin kalaman tunzuri.


Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa hakan ba ya rasa nasaba da wata hira ta kai-tsaye da Kwamanda ya yi a wani gidan rediyo a Kano, inda ya caccaki gwamnatin Kano, tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Kwankwaso da kuma mabiya darikar siyasa ta Kwankwasiyya.


A hirar, Kwamanda ya gargadi gwamnatin jihar kan rade-radin da ake na rusa masarautu biyar a jihar, inda ya yi kira ga jama’a da su fito su yi bore har sai an saka dokar ta-ɓaci a Kano.


Kotun dai ta sanya ranar 29 ga watan Janairu domin sauraren bukatar belin Kwamanda.


Ƙarin bayani na nan tafe

Post a Comment

0 Comments