Kotun Kolin Isra'ila ta yi watsi da shirin Netanyahu na rage ikon alkalai

 Kotun Kolin Isra'ila ta yi watsi da shirin Netanyahu na rage ikon alkalai.




Kotun Kolin Isra'ila ta yi watsi da wani muhimmin bangare na shirin Firaiminista Benjamin Netanyahu na yin garambawul da zai rage karfin iko ga fannin shari'a na kasar.


Alkalai takwas ne suka yi watsi da kudirin yayin da bakwai suka goyi bayansa.


Kudurin, wanda Majalisar Dokokin kasar ta amince da shi a watan Yulin da ya gabata, ya soke ikon da Kotun Koli take da shi na ayyana matakan da gwamnati ta dauka a matsayin marasa kan gado sannan ya rage karfin ikon alkalai.


Majalisar Dokokin Isra'ila mai suna Knesset ta yi kudirin kwaskwarima ranar 24 ga watan Yuli, sannan ta amince da shi.


Sai dai gamayyar jam'iyyun da ke mulkin kasar ta yi fatali da hukuncin na ranar Litinin, inda Ministan Shari'a Yariv Levin ya ce hakan nuna kyama ne ga "hadin kai" da ake bukata a lokacin yaki.


Jam'iyyun hamayya a kasar sun goyi bayan hukuncin, inda shugaban jam'iyyar adawa Yair Lapid ya ce yana mara wa kotun cikakken baya "a rawar da take takawa wajen kare al'ummar Isra'ila."

Post a Comment

0 Comments