Kungiyar Daliban Najeriya NANS shiyyar Kudu Maso Yamma, ta bukaci kamfanin man fetur na kasa, NPL da kada ya yi tunanin kara farashin man fetur zuwa Naira 1,200 ga kowace lita, kamar yadda wasu mutane da kungiyoyi ke yi

 Kungiyar Daliban Najeriya NANS shiyyar Kudu Maso Yamma, ta bukaci kamfanin man fetur na kasa, NPL da kada ya yi tunanin kara farashin man fetur zuwa Naira 1,200 ga kowace lita, kamar yadda wasu mutane da kungiyoyi ke yi.



Kungiyar daliban, a cikin wata sanarwa da ko'odinetan shiyyar, Kwamared Alao John, sakataren kungiyar, Kwamared Sanni Olamide da jami’in hulda da jama’a, Kwamared Bamigboye Oluwadamilola suka fitar, sun ce ra’ayin sake karin farashin da wasu ‘yan kasuwa ke yi bai dace ba. 


NANS ta lura cewa matsayar ta ya samo asali ne a cikin tsananin damuwar da kungiyar ke da shi game da yuwuwar ta’azzara wahalhalun tattalin arziki da ‘yan kasar ke fuskanta.


“Najeriya na fama da kalubalen tattalin arziki, kuma duk wani yunkuri da zai kara dora wa ‘yan kasarta nauyi, zai fuskanci turjiya. 


Shawarar cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin man fetur fiye da yadda ake yi a halin yanzu ta tayar da muhawara a duk fadin kasar. 


“Shugaban NANS shiyyar Kudu maso Yamma mai wakiltar al’ummar Dalibai a yankin, sun dau matsaya kan wannan mataki da aka dauka. Muna jayayya da cewa irin wadannan ayyuka na iya kara tabarbarewar tattalin arzikin talakawan Najeriya wadanda tuni suka fara kokawa da tsadar rayuwa da karancin kudi. " Daliban sun yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu, da ya sake duba wadannan tsare-tsare.


Suna jaddada bukatar gwamnati ta binciko wasu dabaru da za su rage radadin tattalin arziki ba tare da sanya wasu wahalhalu ga jama'a ba.


“NANS shiyyar Kudu-maso-Yamma ta ba da shawarar cewa, maimakon a kayyade farashin man fetur a kan ₦1,200, kamata ya yi gwamnati ta binciko wasu hanyoyin magance kalubalen tattalin arziki ba tare da dora wa jama’a nauyi ba.


Wannan zai iya haɗawa da matakan haɓaka inganci a fannin man fetur, rage cin hanci da rashawa, da haɓaka alhakin kasafin kuɗi. 


“A karshe, NANS shiyyar Kudu maso Yamma tana adawa da shirin karin farashin man fetur. Kiran da muka yi na sake duba manufofin tattalin arziki ya jaddada bukatar samar da mafita da ke ba da fifiko ga jin dadin ‘yan kasa,” in ji kungiyar.

Post a Comment

0 Comments