Kungiyar Taliban ta bayyana kungiyar wahbiyawa ta DAISH (ISIS/ISIL) da cewar kungiya ce ta makiya musulmi da musulunci.
A wata ganawar da suka yi da wakilin Iran a sha'anin kasar Afghanistan, mataimakin firaministan Taliban kan harkokin siyasa Mullah Muhammad Abdul Kabir ya jajantawa kasar Iran bisa harin ta'addancin da aka kai kan mutanen Iran a Kerman. Inda harin yayi sanadiyar rasuwar mutane 90.
Ya bayyana cewar kungiyar DAISH kungiya ce ta yan ta'adda wacce ke neman haifar da rikici da sabani tsakanin Iran ta Taliban. Ya bayyana cewar Afghanistan da Iran zasu hada kai wajen yakar ta'addanci da yan ta'adda.
Mullah Abdul Kabir ya bayyana cewar Taliban ba zata amince yan ta'adda su mayar da kasarss mafakar kai wa makotanta harin ta'addanci ba.
Don haka Afghanistan zata baiwa Iran hadin kai wajen yakar yan ta'adda.
A wani raoton na daban kuma, ministan kiwon lafiya na Afghanistan Mullah Qalandar Ebadi ya roki kasar Iran da ta tamaka wajen horar da jami'an kiwon lafiyar kasarsa, da kuma bai wa likitocin Afghanistan horo na musamman. Mullah Ebadi yayi rokon nasa ne yayin wata ziyarar aiki wacce wasu yan majilisar Shura ta Iran suka kai zuwa kasar ta Afghanistan. Haka zalika ya roki Iran da ta rika karbar daliban Afghanistan domin samun ingattacen ilimi domin fadada ayyukan karatu da karantatwa a Afghanistan
Abu Muhammad
0 Comments