Labarin wata matashiya Mai mabiya Sama da miliyan Daya a TikTok da ta rasa idonta a yaƙin basasar Kamaru

Labarin wata matashiya Mai mabiya Sama da miliyan Daya a TikTok da ta rasa idonta a yaƙin basasar Kamaru.



A shekarar 2018, ƴan awaren Ambazonia sun harbi Naronate Akum a wurin da take sayar da abinci, wanda hakan ya ja ta rasa idonta na dama.

Daga Pauline Odhiambo


A ranar 13 ga watan Yulin 2018, Naronate Akum Ngwa ta kammala sayar da abincinta na rana kenan tana zaune tana hutawa sai wasu maza biyu suka zo suna neman abincin rana.


Sai matashiyar mai shekara 20 ta tashi ta zuba wa mazan biyu shinkafa jellof. Bayan sun kammala cin shinkafar sun tashi za su tafi, sai daya daga cikin mazan ya harbe ta a kai.


"Sai na fadi kasa, amma ban san cewa an harbe ni ba sai da ƴan uwana mata biyu suka rinka ihu suna neman taimako," kamar yadda Naronate ta bayyana.


Wanda ya yi harbin da abokinsa sun gudu daga wurin zuwa lokacin. Sai daga baya ta ji cewa wanda ya harbe ta na daga cikin yan awaren Ambazonia wadanda ke yaki da gwamnatin Kamaru.


Harbin ya faru ne a lokacin da aka saka dokar hana fita a arewa maso yammacin Kamaru, wurin da aka yi ta rikici tsakanin sojoji da kuma ƴan aware.


Rikicin ya fi ƙamari a cikin gari, wanda a nan ne Naronate take zaune da iyayenta da kuma kannenta uku. Domin guje wa wannan rikicin, sai iyalinta suka tafi wani ƙauye wanda ba shi da nisa wanda ake ganin ya fi kusa.

Wuta a cikin kai'


An harbi Naronate da rana, sai dai ba a kai ta asibiti ba sai da aka shafe awanni. Makwaftanta sun rinka tsoro kada sojoji ko kuma ƴan ambazonia su kai musu hari idan suka bar gida a lokacin da aka saka dokar hana fita.


"Ina ta roƙon makwaftana kada su bar ni a kasa na mutu. Na kwanta a can tsawon sa'o'i biyar, inda nake ta roƙonsu su kai ni asibiti," kamar yadda Naronate mai shekara 25 ta shaida wa TRT Afrika.


"Ina cikin tsananin ciwo a lokacin. Ina ta jin kamar an kunna mani wuta a cikin kaina. Abin da nake so a lokacin kawai shi ne na rayu."


A lokacin da maƙwafta suka samu ƙarfin gwiwar kai yarinyar da ta samu rauni zuwa asibiti, sai da suka yi zagaye suka bi wata hanya ta baya domin su guje wa ƴan aware ko kuma sojoji a kan hanyoyi.


"Sai dai muka yi tafiya a cikin daji har muka tsallaka kogi. An yi amfani da rigar sanyina an rufe mani sashen idona da ke zubar da jini, sai dai kwayar idona ta dama ta faɗi amma babu wanda ma ya lura," kamar yadda Naronate ta bayyana.


Ta rasa idonta na dama, kuma da a ce ba a mayar da ita wani babban asibiti nan take a Bamenda ba da ta mutu, inda a nan ta shafe wata biyu tana jinya. Sai da aka yi mata wata tiyata ta fata domin toshe idonta na dama.


Har yanzu akwai wasu ɓurbushin harsashin a kwanyar ta, wanda hakan ke haifar da ciwon kai da matsalar jin ta. Ya zuwa yanzu dai an yi mata tiyatar kunne sau biyu, ba ta yi nasara ba.



'Dushewar mafarki'


Mutane biyu sun nuna sha'awar taimaka wa Naronate domin samar mata kudi don yi mata tiyata, sai dai an sace kudin da aka tara mata. Hakan ya saka ƙaramar yarinyar cikin damuwa.


Bayan ta jure irin damuwar da ta shiga na kokarin karatun aikin lauya, fatan da take da shi na zama lauya ya gushe sakamakon hantararta da ake yi kan rasa idonta daya.


Sakamakon ya damu kan lafiyar kwakwalwa da kuma tsaron ƴarsa, mahaifin Naronate ya soma neman hanyoyin da zai koma kasar Cyprus domin neman mafaka.


Tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022 kasar Cyprus reshen Girka ta karbi buƙatar masu neman mafaka 1,050 daga Kamaru kaɗai, inda mutum 46 kaɗai aka amince da su. Naronate na daga cikin kaɗan waɗanda aka amince da su.


"Na kasa magana a kan labarina a Kamaru sakamakon iyalina suna tsoron ƴan awaren za su iya dawowa domin su kashe ni," kamar yadda Naronate ta bayyana. "Tsawon shekaru, ina shaida wa mutane cewa harsashi ne ya goge ni a kasuwa."



Sake gina rayuwarta


Sai Naronate a karshe ta ji cewa ta aminta da ta bayyana labarinta ga duniya ta hanyar kafafen sada zumunta bayan ta isa Cyprus a 2021, inda har ta samu sama da mabiya mutum miliyan daya a TikTok. Amma har yanzu rayuwar da take zato ta kubuce mata.


Naronate tana rayuwa ne da kuɗin da take samu daga gwamnati tun bayan isarta, inda masu daukar aiki ke kin ɗaukarta aiki sakamakon yadda take.


"Na nemi aiki har a matsayin mai yin sabis a gidan abinci ko kuma mai wanke-wanke. Daya daga cikin masu gidajen abincin ta bayyana mani cewa ba za ta ɗauke ni aiki ba saboda zan iya korar mata kwastamomi," in ji ta.


Ina samun euro 214 a duk wata. Wannan ne kuɗin da nake kashewa a kan abinci da kuma kuɗin da nake kashewa zuwa asibiti," kamar yadda ta yi ƙarin bayani. "Ban san me zan yi ba a wannan lokacin."


Domin ta kara kudin shiga, ta koma yin rigunan saƙa wadanda wani lokaci takan sayar da su har euro 50, amma ba a cika nuna buƙatarsu ba.


"Na koyi saƙa ina firamare, inda muka rinka yin ta a makaranta a matsayin fasaha da ƙirƙira," kamar yadda ta bayyana.


"Wannan fasaha ta taimaka mani yin rigunan saƙa don siyarwa domin na samu ƙarin kuɗin shiga. Zan iya siyan abinci da sauran kayayyaki da wannan kuɗin”


Naronate na shafe kusan kwanaki biyu kafin ta saƙa riga guda ɗaya. Wasu daga cikin kwastamominta a wani lokaci na ba ta kyauta domin nuna jin daɗinsu dangane da baiwarta.


Naronate na da yaƙinin samun aiki mai kyau bayan an yi mata tiyata a nan gaba.


"Samun aiki shi ne babban abin da nake so. Ina sa ran cewa idan na samu aiki, zan iya aiki domin na taimaka wa ƴan uwana," in ji ta.

Post a Comment

0 Comments