Ma'aikatar Ilimi ta jihar kano ta sanar da ranar komawa makaranta.

 Ma'aikatar Ilimi ta jihar kano ta sanar da ranar komawa makaranta, domin fara daukar karatun zango na biyu, ga daliban makarantun kwana dama na jeka ka dawo.




Ma'aikatar Ilimin ta sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama'a na ma'aikatar Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu, inda tace za'a koma makarantar a ranar litinin 8 ga watan janairu sabuwar shekarar da muke ciki ta 2024.


Sanarwar ta kara da cewa daliban makarantun kwana zasu koma ne a gobe lahadi 7 ga wata domin fara daukar darasin, ga daliban makarantun firamare dama na sakandire.


Sanarwar Daraktan ta kuma bukaci iyaye dama wakilan daliban suyi biyayya ga dukkan ka'idojin komawa makarantar, inda yace zasu dauki mataki ga daliban da suka bijirewa umarnin.


Haka kuma sanarwar ta yabawa gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusif, a bisa yadda ta gyara motocin kai yara makaranta, domin daliban suji dadin zuwa koyon karatun.


A karshe sanarwar ta ambato kwamishinan ilimi na jihar kano Alhaji Umar Haruna Doguwa, na fatan malamai dama daliban zasuyi karatun zango na biyun cikin nasara,tare da jaddada sanya idanu akan yadda malaman makarantun jihar suke gudanar da ayyukan su.

Post a Comment

0 Comments