Mace zata iya yin Zina Don taci abinci inji prof Makari, maganar Shi Tsantsan Ilimi ne inji Sheriff Ahmad Mukaddam.
Naga Jahilan Yan kungiyar suna ta yawo da maganar Prof. akan tsanain buƙata na iya halartawa mace bayar da kanta dan taci Abinci.
Mutanennan sun arhanta harkar ilimi sun sa kowa yanzu jinsa yake malami. yanzu inba Jahilci ba wannan Mas'alar ai tafi rana fitowa ga dukkan ƙaramin Ɗalibin ilimi ma.
Kiyaye rai حفظ النفس yana daga cikin Maqasid na shari'a, kuma buƙatar kiyaye shi tana iya sakawa a sarayar da shi kansa ran dan samun kuɓutar wasu da yawa.
kuma in ana maganar Larura toh duk wani Abu wanda yake haramun ze iya zama halal, daga ciki har firta shirka a baki da kuma sakin baki ga Allah da Annabi S.A.W, wannan yasa da Ammaru matsawar kafirari ta saka ya zagi Allah da Annabi S.A.W dan kuɓuta akace babu komai har aya ta sauka ta wanke shi.
مَن كَفَرَ بِاللَّهِ مِن بَعْدِ إِيمَانِهِ إِلَّا مَنْ أُكْرِهَ وَقَلْبُهُ مُطْمَئِنٌّ بِالْإِيمَانِ وَلَٰكِن مَّن شَرَحَ بِالْكُفْرِ صَدْرًا فَعَلَيْهِمْ غَضَبٌ مِّنَ اللَّهِ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ.
Wannan ne ya saka Malaman Usulu suke da ƙa'idar الضرورات تبيح المحظورات wato larura na halatta dukkan wani Abu wanda yake haramun.
Shan jini Haramunne cin Mushe haramunne cin namna Alhanzir haramunne amma Allah a cikin Alqur'ani yace in tsananin buƙata takai ka ka iya ci, saboda kare ran da shine gaba da komai.
إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيْكُمُ الْمَيْتَةَ وَالدَّمَ وَلَحْمَ الْخِنزِيرِ وَمَا أُهِلَّ بِهِ لِغَيْرِ اللَّهِ ۖ فَمَنِ اضْطُرَّ غَيْرَ بَاغٍ وَلَا عَادٍ فَلَا إِثْمَ عَلَيْهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Akwai Sahabin da janaba ta kamshi ana tsananin sanyi kuma ya nada ciwo, ya tambayi mutanen sa shin babu wata hanya inba wanka ba !? suka ce ai indai akwai ruwa wanka kawai zeyi, sai yayi wanka da ruwan sanyi, ya mutu. Annabi S.A.W yace: Sun kashe shi Allah ya tsine musu, meyasa bazasu ce yayi taimama ba.
Yanzu ko haɗari za'ayi me tierla ya taho me mashin ya taho motar ka ta tawo, kuma dole sai ka zaɓi ɗaya, kodai ku da kuke cikin mota a ƙalla misali ku 5, shi kuma me mashin shi kaɗai, toh da kayi kan tirela ku mutu gaba ɗaya gwara me mashin shi kaɗai ya mutu wannan shine dai-dai.
A dinga karatu wallahi sai ƙaryar karantar Islamic studies amma masu yare ma su fiku fuskantar addini!
Sheriff Ahmad Mukaddam ✍
0 Comments