Makafi Sunyi Waliman Cika Shekaru 12 Da Sheikh Ibrahim Zakzaky Yasiya Musu Gida

Makafi Sunyi Waliman Cika Shekaru 12 Da Sheikh Ibrahim Zakzaky Yasiya Musu Gida 



Yau Asabar 20/1/2024 , Sarkin Makafin Tudun Wadan Zariya ,yakira kwarya kwaryan walima na cikan shekaru 12 da Sheikh Zakzaky yasiya musu Gida .


Tunda farko madakin Makafin Tudun Wadan yayi ma mahalata tuni dacewa a wancan Lokacin sun sha kai komo na niman wanda zai saya musu gida amma suka rasa, shi dakan shi yarabama mutane takardan niman taimakon sama da mutum talatin na asiya musu gidan dazasu zauna amma hakan bai samu ba.


Shima Marafan Makafin yace bazai taba manta randa Sarkin Makafin yajagorancesu zuwa ga Sheikh Zakzaky a Gidan sa dake Gyallesu kuma cikin girmawa da karramawa, Sheikh Zakzaky ya karbesu hannu biyu ya amsa bukatun su ya siya musu gidan.


Anasa jawabin Sarkin Makafin Tudun Wadan Zariya Malam Dauda yace saboda Wannan abin alheri da faranta zukatan su da sheikh Zakzaky yayi ne, yau Shekaru 12 dai dai suka shirya walima don nuna godiyyr su ga Malam . Yakara dacewa duk da basuda abinda zasu baiwa Sheikh Zakzaky saidai addu'a, yace hatta lokacin waki'ar Buhari sukan hadu lokaci bayan Lokaci sunaiwa Malam Zakzaky addu'a.


Sarkin Makafin yace yayi burin wannan walima dasuka shirya akwai Farfesa Abdullhi Dalladi saboda bazasu manta randa shine Sheikh Zakzaky ya aiko da kudin siyan Gidan ba.


Wakilin yan uwa Musulmai Almajiran Sheikh Zakzaky na Tudun Wadan Zariya Alaramma Malam Sani, wanda aka bukaci yace wani abu a wurin yace lallai bazai manta Lokaci dasukaje suka fadiwa Sarkin Tudun Wada marigayi Sarki Bulaki cewa Sheikh Zakzaky yasiwa makafi gida ba . inda yayi murna kwarai yakara dacewa antabin mutane masu hali su taimaki makafin su siya musu gida abin yaci tura..


Andai addu'a sosai ga su sheikh Zakzaky na Allah yakara musu lafiya da kariya , akarshe aka raba walima aka sallami jama'a, Andai gabatar da Waliman ne a Gidan nasu dake Dikko Road (layin makafi) Tudun Wada Zariya kuma da damansu sun halarta .


Zaria media

20/1/2024.

Post a Comment

0 Comments