Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya gana da Haniyeh jagoran siyasa na Hamas kan tsagaita wuta a Gaza

 Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya gana da Haniyeh jagoran siyasa na Hamas  kan tsagaita wuta a Gaza



Manyan jami'an biyu sun tattauna kan batun tsagaita wuta nan-take a Gaza da kai karin kayan agaji yankin da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma samar da kasashe biyu masu 'yancin kansu.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya gana da shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas, Ismail Haniyeh, a cewar wasu majiyoyi na diflomasiyyar Turkiyya.


Fidan and Haniyeh sun tattauna ranar Asabar kan batun tsagaita wuta nan-take a Gaza da kai karin kayan agaji yankin da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma samar da kasashe biyu masu 'yancin kansu.


Hare-haren da Isra'ila take kai wa a Gaza sun raba kashi 85 na mutanen yankin da muhallansu a yayin da ake cikin tsananin rashin abinci da ruwa mai tsafta da magunguna, sannan an rusa kashi 60 na gine-ginen yankin, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.


A watan Oktoban da ya wuce, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna da Haniyeh bayan Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a Gaza inda ya tabbatar masa cewa Ankara zai kai kayan agaji Gaza sannan za a dauko wadanda suka jikkata a yankin domin kawo su Turkiyya su yi jinya idan akwai bukatar hakan.


Shugaba Erdogan ya jaddada cewa ba za a samu dauwamammen zaman lafiya a yankin ba sai Falasdinawa sun samu kasa mai zaman kanta kamar yadda take a 1967 wacce Birnin Kudus zai zama babban birninta.


Erdogan ya kara da cewa Turkiyya za ta ci gaba da fafutuka domin ganin an samu zaman lafiya a yankin.


Isra'ila ta kaddamar da hare-hare babu kakkautawa ta sama da ta kasa a Gaza tun bayan da Hamas ta kai mata barin ba-zata, wanda Tel Aviv ya ce ya kashe akalla mutum 1,200.


Ta kashe Falasdinawa akalla 24,927, galibinsu mata da kananan yara, sannan an jikkata mutum 62,388, a cewar hukumar lafiya ta Falasdinu.

Post a Comment

0 Comments