Mr. Luke Leyland yace ko a haka ya kafa Tarihi, duk da dai abokin Damben nasa ya barshi da tabo a fuska, kuma ya kusan karya masa karan hanci.
Ya Fadi Hakan ne a wata tattaunawa da sukai da Katsina city news.
Ana cigaba da bayyana zafafan ra'ayoyi game da fafata wasan damben gargajiya da akayi tsakanin wani Bature daga kasar Ingila mai suna Mr. Luke Layland wanda ya yi takanas zuwa Najeriya domin yin Damben aka haÉ—a shi da wani matashin É—an dambe daga Arewacin Najeriya mai suna Shagon Dan Zuru a filin dambe da ke garin Katsina da yammacin jiya Asabar,
To sai dai Shagon Dan Zuru ne ya samu nasara a kan Baturen bayan ya yi masa dukan kawo wuƙa wanda dakyar aka raba wasan.
Muhammad Yamai yayi mana sharhi akai inda yake bayyana ra'ayinsa da cewa "Gaskiya Organisers na dambe tsakanin Baturen Ingila da Dan Nigeria wanda akayi a Katsina basu da courtesy da diplomacy, kuma basu iya aiki ba.
Irin wannan ceremonial wasan ba'a yinsa da gaske. Ana kawo wanda Baturen zai iya fin qarfinsa ne sai a hadasu damben. A hakan ma za'a ja kunnen shi Ɗan damben da Baturen kan cewa yariƙa yin lako-lako don Baturen yayi galaba akansa."
A cewar Yamai "Amma kawai sai basuyi haka ba suka kawo wani Baƙauyen Ɗan Dambe ya rinƙa suburbuda da sharara wa Baturen naushi sai da ya galabaitar dashi yaji masa ciwo a fuska."
Gaskiya basu kyauta wa Baturen nan ba, amma ku ya kuka gani?
0 Comments