Mujahidan Falasdinu sunyi jinjina ga dakarun Ansarullah na yamen.

Mujahidan Falasdinu sunyi  jinjina ga dakarun Ansarullah na yamen.



Muna yin Allah wadai da ci gaba da kai hare-haren wuce gona da irin na Amurka da Birtaniya da Sahayoniya, wanda ya zo ne domin kare ‘yan ta’addan sahyoniyawan da suke aikata kisan kiyashi a zirin Gaza, kan ‘yan’uwan Yemen.

Muna sabunta matsayinmu ga Yaman Muna  kaunar al'ummarta, kuma muna darajta su gami da  riko da matsayinsu na tarihi na goyon bayan al'ummar Palastinu da tsayin daka da kuma watsi da zalunci, dukda kawanya da wuce gona da iri da ake yi musu.

Dukda makirce-makirce, zalunci da wara da suke fuskanta. Harkar Ansarallah da mayaka sojojin Yaman na ci gaba da yin riko da kakaba takunkumin hana zirga-zirgar jiragen ruwa kan kasuwancin sahyoniyawa. 

Suna gudanar da aikin soji mafi daraja don kawar da zaluncin da ake yi wa al'ummar Gaza, wadanda ake yi wa kisan gilla, azabtarwa da yunwa da kawanya bisa la'akari da gazawa da hadin kan cibiyoyin kasa da kasa da gazawarsu wajen kare su ko rage musu radadi. 

Zaluncinsu Gwamnatin Amurka ta dage kan zubar da jinin al'ummarmu ta Larabawa da Musulunci, tare da hada kawance don kare sahayoniya, da take hakkin al'umma da kuma ikon mallakar filayensu ta hanyar yin shiru da rashin aiki. 

Muna kira da a karfafa hadin kan dukkanin al'ummar kasarmu masu 'yanci don tinkarar hare-haren wuce gona da iri na Amurka da kuma matsa lamba kan muradun 'yan ta'adda har sai an karya lagon da ake yi a Palastinu, Yemen da sauran al'ummarmu. 

Mujahidan Falasdinu 


Post a Comment

0 Comments