Netanyahu na son rufe wasu ma’aikatun Isra’ila don rage kashe kudi.

 Netanyahu na son rufe wasu ma’aikatun Isra’ila don rage kashe kudi.

  Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu


Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya soma tunanin kulle wasu ma’aikatun gwamnatin kasar a yunkurin rage kashe kudi, kamar yadda kafar watsa labarai ta kasar ta bayyana a ranar Litinin.


Netanyahu na tunanin ci gaba da kasancewa da wasu ministoci a gwamnatinsa wadanda ba su da ma’aikatu, don guje wa rikicin kawancen da za a iya fuskanta, kamar yadda gidan rediyon Reshet Bet ya bayyana.


Ana sa ran gudanar da taro na musamman a ranar Alhamis mai zuwa domin tattaunawa kan yiwuwar rufe wasu kananan ma’aikatun kasar

Post a Comment

0 Comments