Pakistan ta kai harin ramuwar gayya a Iran

Pakistan ta kai harin ramuwar gayya a Iran.

Tehran ta ce mata uku da kananan yara hudu ne suka mutu bayan harin makami mai linzami da Pakistan ta harba zuwa Sistan-Baluchistan a wani sabon rikici da ya barke tsakanin kasashen biyu masu karfin soji.



Pakistan ta kaddamar da jerin hare-hare a Iran kan kungiyar ta'addanci ta Balochistan Liberation Army (BLA), bayan ikirarin Tehran na kai hari kan wani sansanin 'yan ta'adda a lardin Balochistan na Pakistan.


Pakistan ta mayar da martani kan hare-haren da Tehran ta kai "ba bisa ka'ida" a Iran da safiyar ranar Alhamis.


''Zan iya tabbatar da cewa mun kai wasu jerin hare-hare kan kungiyoyin 'yan ta'adda masu adawa da Pakistan da aka gano su a Iran,'' a cewar wata majiyar leken asiri da ba a ba ta izininyin bayani ga manema labarai ba ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP, inda ta kara da cewa sanarwar gwamnati za ta biyo baya.


"An ji karar fashewar wasu abubuwa a yankuna da dama da ke kusa da birnin na Saravan," a cewar kamfanin dillacin labarai na IR, yana mai ambato wani jami'i daga lardin Sistan-Baluchestan inda birnin yake.


Mutane da dama sun mutu a Iran


Iran ta tabbatar da cewa an kai jerin hare-hare da makamai masu linzami daga Pakistan zuwa wani kauye da ke kan iyaka da lardin Sistan-Baluchistan, kamar yadda wani jami'in tsaron Iran a lardin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na YoungJournalist Club.


Jami'in ya kara da cewa akalla mata uku da kananan yara hudu ne suka mutu a daya daga cikin harin fashewar, inda ya bayyana cewa daga cikin dukka babu wani dan kasar Iran.


Hakan na zuwa ne bayan da Iran ta kai wasu hare-hare kan "maboyar 'yan ta'adda" da ta ce an gano a yammacin ranar Talata a Pakistan - harin da Islamabad ta ce ya kashe yara biyu tare da raunata wasu 'yan mata uku.


Harin makami mai linzami da na jirage marasa matuka sun fada kan mayakan kungiyar Jaish al Adl a Pakistan, kamar yadda gwamnatin Iran ta yi ikirari.

Post a Comment

0 Comments