Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce jami’anta sun kama wasu mutane uku da ke damun jama’a a jihar.

 Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce jami’anta sun kama wasu mutane uku da ke damun jama’a a yankin Shasha, Akowonjo da ke jihar. 

       Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin.


Mutanen, Julius Sarn mai shekaru 43, Isiaka Kabiru mai shekaru 16, da Ajewole Ajugba mai shekaru 42, an kama su ne bisa laifin yin watsi da dokokin da ake da su na yin amfani da lamuni a bainar jama'a a jihar.


 Rundunar ta bayyana hakan ne a ranar Asabar da ta gabata a shafinta na X a cikin wata sanarwa da jami’in ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ya fitar. 


Hundeyin ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne da misalin karfe 12:23 na rana. A kan titin Abatti, Shasha, inda suke shirya shagalin Wani biki.

Post a Comment

0 Comments