Sadiya Farouq ta kai kanta ofishin EFCC Ana zargin wani dan kwangila a ma’aikatarta da almundahanar sama da naira biliyan 37.

 Tsohuwar Ministar Ayyukan Jin Kai ta Nijeriya Sadiya Umar Farouq ta gabatar da kanta a gaban hukumar EFCC a Abuja babban birnin Nijeriya.




Ana zargin wani dan kwangila a ma’aikatarta da almundahanar sama da naira biliyan 37.


Tun a makon da ya gabata ne ya kamata tsohuwar ministar ta gabatar da kanta a gaban hukumar, sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar da ba ta je ba.


Sai dai a safiyar Litinin tsohuwar ministar ta fitar da sanarwa a shafinta na X inda ta sanar da zuwanta hukumar.


“Bisa radin kaina, na isa hedikwatar hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zango kasa (EFCC) domin karbar goron gayyata domin karin haske dangane da wasu lamura wadanda ake hukumar ke bincike a kai,” kamar yadda ta bayyana a shafin X.


Sai dai a kwanakin baya, tsohuwar ministar ta wallafa wani sako a ranar 26 ga watan Disambar 2023 inda take nesanta kanta daga duk wasu rahotanni da ke nuna cewa EFCC na bincike a kanta inda hasalima ta yi zargin ana kokarin bata mata suna.

Post a Comment

0 Comments