SCSN ta ce ta dawo daga rakiyar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu inda ta ce an yi watsi da muradun Musulman ƙasar.

SCSN ta ce ta dawo daga rakiyar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu inda ta ce an yi watsi da muradun Musulman ƙasar.



Majalisar ƙoli kan harkokin shari'ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta ce ta dawo daga rakiyar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu inda ta ce an yi watsi da muradun Musulman ƙasar.


Majalisar ta bayyana haka ne a wajen taron da ta kira na kwanaki biyu a Abuja domin nazari kan abubuwan da suka biyo bayan zaɓen 2023 a Najeriya.


Babban magatakardar majalasar, Nafiu Baba Ahmed ya shaida wa manema labarai cewa majalisar ta kira taron ne saboda sauraron ƙorafe-ƙorafe na ɓangarori daban-daban da mutane ke da shi sakamakon abubuan da suka biyo bayan zaɓen 2023 a Najeriya.


Me zaku ce?

Post a Comment

0 Comments