Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a cikin raha ya tuna wa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari cewa a yanzu ba zai iya koma wa Nijar ba kamar yadda ya taba fada a baya.

 Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a cikin raha ya tuna wa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari cewa a yanzu ba zai iya koma wa Nijar ba kamar yadda ya taba fada a baya.

“Na tuna Buhari ya taba cewa idan magoya bayansa da abokansa suka hana shi samun isasshen hutu a Daura, zai gudu zuwa Nijar.To, kamar yadda kuka sani, ba zai iya tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar ba, saboda rufe iyakokin kasa da aka yi.’’

Tinubu ya fadi hakan ne a taron kaddamar da wasu litattafai biyu da aka yi a kan rayuwar Buharin a ranar Talata a Abuja.

Post a Comment

0 Comments