Tinubu ya amince a biya Super Eagles da wasu 'yan wasan Nijeriya bashin biliyan 12

Tinubu ya amince a biya Super Eagles da wasu 'yan wasan Nijeriya bashin biliyan 12

Biyan bashin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Super Eagles ke shirin wasa a gasar AFCON wadda za a yi a Ivory Coast.



 Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince a biya bashin naira biliyan 12 da kungiyoyin wasannin Nijeriya suke bi, daga ciki har da kungiyar Super Eagles.


Daga cikin bashin da za a biya, har da kudaden da manyan kociya ke bi na albashinsu wanda ya kai watanni 15. Haka kuma akwai alawus-alawus da kuma alkawura da aka yi wa manyan ‘yan wasa maza da mata da ‘yan kasa da shekara 20.


Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da babbar kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya Super Eagles ke shirin soma wasa a gasar AFCON wadda za a fara a cikin watan nan na Janairu.


Tun a bara sai dai kungiyar ta Super Eagles ta yi barazanar kin buga gasar ta AFCON kan kin biyanta hakkokinta.


Masu sharhi dai sun sha danganta rashin rashin karsashi da a wasu lokuta ‘yan wasan na Nijeriya ke nunawa a wasannin nasu da rashin biyansu hakkokinsu da suka dace wanda hakan ke kara sanyaya musu gwiwa.

Post a Comment

0 Comments