Tinubu ya dakatar da Ministar Ma'aikatar Jinkai Betta Edu.
An dakatar da Minista Edu ne kwana guda bayan shugaban kasar ya umarci a gudanar da bincike a kanta bisa zargin badakalar naira miliyan 585.
Betta Edu
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya dakatar da Ministar Ma'aikatar Jinkai Betta Edu kan zargin badakalar miliyoyin kudade.
An dakatar da Minista Edu ne kwana guda bayan shugaban kasar ya umarci a gudanar da bincike a kanta bisa zargin badakalar naira miliyan 585.
Shugaba Tinubu ya bai wa EFCC umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan duk wasu hada-hadar kudi na Hukumar Kula da Ayyukan Jinkai ta Nijeriya
Haka kuma shugaban kasar ya bayar ga umarni ga babban sakataren hukumar ya karbi ragamar jagorancin hukumar, tare da bukatar ministar kan ta bai wa hukumomi hadin kai domin gudanar da bincike a kanta.
An yi ce-ce-ku-ce tun daga makon da ya gabata bayan wasu takardu sun nuna cewa Ministar Jinkai Betta Edu ta bayar da umarni ga Akanta Janar ta Nijeriya ta tura naira miliyan 585 ga asusun wata mata mai suna Onlyelu Bridget Mojso a matsayin tallafi na shirin bayar da kudi ga marasa galihu.
Sai dai Akanta Janar ta Nijeriya Dakta Oluwatoyin Madein ta ce ofishinta ba ya biyan kudi a madadin ma’aikatu da hukumomin gwamnati kan ayyukan da suke aiwatarwa.
Bayan da ce-ce-ku-cen ya soma yawa sai Shugaba Tinubu ya bayar da umarni a soma bincike kan wannan lamarin inda daga aka dakatar da ita.
Karin labarai
0 Comments