Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa za su hada kai domin yakar ta'addanci

 Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa za su hada kai domin yakar ta'addanci.



An kashe sojojin Turkiyya tara a wani hari da 'yan ta'addan PKK suka kai a arewacin Iraki a ranar Juma'a.


Shugaban Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun tattauna ta waya kan yadda za su dakile ta’addanci.


Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi magana ta waya da Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan na Hadaddiyar Daular Larabawa, kamar yadda Ma’ikatar Sadarwa ta Turkiyya ta tabbatar a wata sanarwa.


A lokacin wayar, Al Nayhan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Erdogan kan wani harin ta’addanci da aka kai kan sojojin Turkiyya a arewacin Iraki, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojojin Tutkiyya tara.


Operation Claw-Lock


'Yan ta'addar PKK suna yawan fakewa a arewacin Iraki domin shirya kai hare-haren a cikin Turkiyya ta hanyar tsallaka iyaka.


A watan Afrilun shekarar 2022 ne Turkiyya ta kaddamar da Operation Claw-Lock domin kai hari kan maboyar 'yan ta'addar PKK a yankunan Metina, Zap, da Avasin-Basyan na arewacin Iraki kusa da kan iyakar Turkiyya.


Kafin haka dai an kaddamar da Operation Claw-Tiger da Claw-Eagle a shekarar 2020 domin kakkabe 'yan ta'adda da ke buya a arewacin Iraki da kuma shirya kai hare-hare a kan iyakokin kasar Turkiyya.


A cikin sama da shekaru 35 da PKK ta dauka tana ta’addanci a kan Turkiyya, kasashen Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana PKK a jerin sunayen 'yan ta'adda. Kungiyar ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40,000 da suka hada da mata da yara da jarirai.

Post a Comment

0 Comments