Uwar gidan Gwamnan jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Radda ta dauki nauyin tallafawa rayuwar wata yarinya wadda dangin mahaifin ta ke son aurar da ita ga barwon daji
Dangin mahaifan wata yarinya yar shekara 15 mai suna Amina Sulaiman dake karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina sunyi yunkurin aurar da ita ne ga wani barawon daji wanda sanadiyar haka ne, yarinyar ta ce da ta aure shi ya ciyar da ita da haramun gara ta gudu ta tafi ta bar garin ko kuma ta tafi neman mahaifiyar ta dake jihar Kaduna.
Dangin mahaifin yarinyar sunyi yunkurin aurar da ita ga barawon dajin ba don suna so ba, sai don tursasa su da barawon dajin ya yi da kuma yi masu barazanar zai kai masu hari.
Ganin yunkurin da dangin mahaifinta keyi ne, ya sa ta barin garin nasu da niyyar tafiya neman mahaifiyar ta dake Kaduna wanda ita kanta bata san inda zata gano ta ba.
A lokacin da take yunkurin tafiya ne, ta fada hanun hukumar JTF na jihar Katsina inda sukai mata tambayoyi.
Ahmed Ibrahim Sarkin matasa wanda shine kwamandan na yan JTF ya dauki yarinyar zuwa wajen iyalen shi sannan shi ma shugaban karamar hukumar Danmusa Alhaji Dangi Abbas suka yi kokarin taimaka mata.
A lokacin da take jawabi Uwar gidan Gwamnan jihar tace taga faifan bidion hirar yarinyar da aka yi da ita shine ta bukaci a kawo mata domin ta yi mata tambayoyi tare da tallafa ma rayuwar ta.
Hajiyar Zulaihat ta dauki nauyin tallafawa rayuwar yarinyar.
Ita ma Hajiya Jamila Abdu Mani mai baiwa Gwamnan jihar Katsina shawara kan harkokin ilimin ya ya mata tace office din zai yi kokari wajen tallafa yarinyar dama saura duk wasu masu irin wanan kalubalen.
An gudanar da taron a gidan gwamnatin jihar da yammaci yau Juma'a 26 Janairu 2024.
0 Comments