Wanene Mohammed Deif ?.

 Wanene Mohammed Deif ?.



Muhammad Deif wani nakasasshen mayaki ne da aka haifa a sansanin ’yan gudun hijira da ke birnin Gaza a kasar ta Falasdin.


Tun a shekarar 2002 ce Deif yake jagorantar bangaren sojin na Hamas, wato rundunar Qassam.


Akalla sau bakwai yana tsallake rijiya da baya a yunkurin da kasar Isra’ila take yi na kashe shi, inda daga cikin hare-haren da aka kai masa din aka kashe matarsa da ’ya’yansa, ciki har da jariri. Haka kuma ya rasa idonsa guda daya, da hannu daya da kafa daya.


Kamar Sheikh Ahmed Yassin, wanda shi ma wani nakasasshen jagora ne na Hamas da harin jirgin saman Isra’ila ya kashe a shekarar 2004, shi Deif mai shekara 57 ya kasance yana jagorantar Rundunar Qassam din a keken guragu na tsawon shekara 20.


Daya daga cikin manyan Hamas a lokacin da yake siffanta Deif, wanda sunansa ke nufin bako a harshen Larabci saboda kasancewarsa mai yanayi da makiyaya na yawan yin kaura domin guje wa Isra’ila.


Ba kamar sauran jagororin kasar Falasdin din ba, shi Deif ba ya sha’awa kuma ba ya shiga cikin rikicin shugabancin kasar, inda shi ya fi mayar da hankalinsa a kan yaki da Isra’ila, kamar yadda masana suka bayyana.


A karshe-karshen shekarar 2010, Deif ya rubuta wata makala inda a ciki ya bayyana wasu daga cikin muradun kungiyar kamar yadda shi yake so, inda a ciki ya ce, “Kasar Falasdin za ta cigaba da zama mallakinmu, ciki kuwa har da Kudus da Masallacin Kudus da biranenta da kauyukanta tun daga tekun maliya zuwa tekun Jordan, tun daga Arewa zuwa Kudu. Ke (Isra’ila) ba ki da hakkin mallakar ko inci daya a ciki.”


Har yanzu babu cikakken bayani a game da Deif. Daga cikin abubuwan da ba a sani ba a game shi har da iyayensa da kuma yaya kuruciyarsa ta kasance.


Daga cikin alamomin kasancewarsa mai tsananin sirri akwai rashin samun hotonsa mai kyau har yanzu. Sashen leken asirin Isra’ila ya yi amannar cewa asalin sunansa Mohammed Diab Ibrahim al-Masri.


Duk da cewa suna shan suka na gaza ganowa tare da dakila lokacin da Hamas ke shirye-shiryen kai hare-hare, sashen na leken asiri ya bayyana cewa ‘yan uwan Deif suna cikin mayakan Falasdin na Fedayeen, wadanda a shekarun 1950s suka fafata da Isra’ila.


Kamar wasu jagororin Falasdinawa da dama wadanda suka shiga cikin fafutikar kwatar ‘yancin kasar tun daga jami’a, shi ma Deif ya fara alaka ne da kungiyar Hamas tun dagak Jami’ar Musulunci ta Gaza.


Deif ya shiga Rundunar Qassam ce wadda aka kirkira jim kadan bayan yarjejeniyar ta Oslo a karkashin jagorancin Yahaya Ayyash da Adnan al-Ghoul wadanda suka kasance biyu daga cikin manyan masu tsare-tsaren Kungiyar Hamas kafin kasar Isra’ila ta kashe su.


Deif ya shiga cikin tsare-tsaren rundunar da dama ciki har da hare-hare da suka yi sanadiyar mutuwar sojojin Isra’ila da dama a cikin kasarsu. Haka kuma Deif yana cikin wadanda suka jagoranci hare-haren da Falasdinawa suka kai wa Isra’ila a fafatikar Intifada ta biyu a tsakanin 2000 zuwa 2005.


® Mahadi Umar Imam ✍️

Post a Comment

0 Comments