Ya kamata mutane su daina biyan kuɗin fansa - Badaru

 Ya kamata mutane su daina biyan kuɗin fansa - Badaru

       Ministan tsaron Najeriya Mohammed Badaru Abubakar


Ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya ce lokaci ya yi da za a daina biyan kuɗin fansa saboda haka ne kaɗai hanyar kawo karshen masu garkuwa da mutane.


Ministan ya bayyana haka ne a taron majalisar zartaswa ta ƙasa da aka gudanar a yau Laraba.


Ya ce shugaban ƙasa ya bai wa dukkan hafsoshin tsaro goyon baya da ta kamata don ganin an kawo karshen garkuwa da mutane da ya yi ƙamari a ƙasar.


Ministan tsaron ya ce dokar Najeriya ta hana bayar da kuɗin fansa kuma bai kamata mutane su rika biyan kuɗi ba saboda ba shi da amfani.


"Babbar matsalar ita ce yadda mutane ke fitowa a kafafen yaɗa labarai suna neman taimako, har a zo a tara domin biyan fansa. Hakan bai dace ba.


"Idan muka daina biyan kuɗin fansa, sannu a hankali ayyukan masu garkuwa da mutane zai zama tarihi," in ji Badaru.


Dangane da yadda rashin tsaro ke ƙara ta'azzara a Abuja, babban birnin ƙasar da kuma garkuwa da mutane da ake yi a yankunan gefen birnin, Ministan ya ce ayyukan da ake yi na korar ƴan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya shi ya sa suke ta ƙaura da guje-guje.


"Shugaban ƙasa ya ba mu umarni tare da duka hafsoshin tsaro, ya kuma ce lallai a je a tsayar da wannan abu da ke faruwa. Kuma mun sa ƙaimi don ganin mun kawo ƙarshensu," in ji Badaru.


Ya ce ana ci gaba da fatattakar ƴan bindigar a jihohin Zamfara da Borno don ganin an daƙile ayyukansu.

Post a Comment

0 Comments