Yacce aka gudanar da bikin tunawa da Haihuwar imamu Ali a Tehran Iran.

 Yacce aka gudanar da bikin tunawa da Haihuwar imamu Ali a Tehran Iran.


Daga:- Ahmad Muhammad Mashi.

A yau Alhamis 13Rajab/25Jan24, Yan'uwa na Dandalin (Academic Forum) dake Tehran da ya hado dukkanin jami'oin dake chikin Birnin na Tehran ne suka hadu domin gabatar da Mauludin Amiral Muminin (Ali bn Abu Dalib da Sayyida Fatimah). 

Anfara da bude taron da Addu'a, sai Karatun Alkur'ani don neman albarka, bayan nan sai aka tsunduma kai tsaye chikin agendodi, inda aka gabatar da Rero wakokin yabo daga Yan'uwa Sha'irai. 

Nan take aka gabatar da Babban bako mai jawabi wanda DR. Ne kuma hujjatul Islam wal'muslimin ne dake koyarwa a Jami’ar koyon aikin likitanchi dake Tehran. 

DR. Yafara jawabin ne da jindadin sa game da yadda yaga almajiran Sayyid sunyi kokarin hada taron, abun burgewa kuma shine kowa da dogayen kaya na al'ada. 

Dayake jawabin ya nuna yadda Allah yaiwa wannan Al'umma riko da Addini fiyeda kowane Al'umma (injishi). 

"Karfin imanin wannan Al'umma yafi ka kwatanta shi da na Sahabban Manzon Allah!, Yakawo misalin yadda mutane suka dake lokacin yakin IRAN da IRAQ a masallacin juma'a na Tehran ta yadda ya tada Bomb! A masallacin juma'a na Tehran a lokacin Sayyid Khamenei ne ke gabatar da kuduba a wurin duk da munanan raunuka da karkashe bayin Allah amma mutane sunki subar wajen, kuma Sayyid Khamenei yachigaba khudbarsa a wurin dukda yanayin da ake chiki. Injishi. 

Yache yayin da Sahabban Manzon Allah yana Huduba a mimbari suke watsewa subarshi sutafi chin kasuwa ko wasa kamar yadda yazo a chikin Suratul JUMU'A. 

 Bayan jawabi an gabatar da kachichi kachichi (Quiz), gami da yanka Cake Sannan aka raba kyauta ga wanda sukai nasara a Quiz. 

Anyi walima akai addu'a aka sallami kowa. 












📸Ahmad Mashi

Post a Comment

0 Comments