Yacce darajar dala ke dada hauhawa, yayinda naira ke ci gaba da durƙushewa.


 Yacce darajar dala ke dada hauhawa, yayinda naira ke ci gaba da durƙushewa.


Darajar kuɗin Najeriya naira na ci gaba da durƙushewa yayin da farashin dala ke sake hawa inda a safiyar ranar Juma'a ake sayar da dala daya kan naira 1,360 a kasuwannin canji da ke Abuja, babbar birnin taraya, kamar yadda, Alh Abbdullahi Abubakar, shugaban ƴan canji na Abuja ya shaida mana.


Alhaji Abubakar ya ce tun makon da ya gabata har zuwa yanzu, farashin dala bai sauka ba.


"Tun da aka shiga wannan sabuwar shekarar, farashin dala ke hauhawa, tun ana siyar da dalar kan naira 1,215, a yau Juma'a, farashin dala ta haura zuwa naira 1,360 a kan ko wacce dala kasuwan bayan fage da ke Abuja."


Abubakar ya ce wasu dalilan da ke haifar da durƙushewar naira kan dala sun haɗa da rashin sa ido daga ɓangaran gwamnati da kuma mutane da dama da ke siyan dalar suna ajiye wa a matsayin kadara.


Ya ce ga dukkan alama, idan har gwanati ba ta tashi tsaye ba, dalar za ta ci gaba da tashi.


A legas kuma, Liman, wani ɗan canji a can ya ce dalar ta tashi itama a kan naira 1,360, a safiyar yau, Juma'a, amma ya ƙara da cewa yanzu da rana dalar ta fara ƙasa inda ta sauka zuwa naira 1355.


Ya ce a jiya Alhamis, an rufe dalar a kan naira 1,349.


A Kano kuma, Yusuf Nabahani, tsohon shugaban kasuwan ƴan canji, shi ma yace kusan kullum farashin dalar ƙaruwa ya ke yi inda ya ce a safiyar yau, Juma'a, dalar ta tashi a kan naira 1,353.


Ya ce a jiya Alhamis, an siyar da dalar kan naira 1,350


Me ya sa darajar naira ke daɗa karyewa?

Mummunar faɗuwar darajar naira a tarihi

Post a Comment

0 Comments