Yadda ake gane labaran karya da ake yadawa a intanet.

 Yadda ake gane labaran karya da ake yadawa a intanet.



Labaran karya ba sabon lamari bane, Duk da daukakar da ya samu sakamakon zaben shugaban kasa na 2016, lamarin ya kasance tun lokacin da dan Adam ya fara yada bayanai – daga magana zuwa jaridu na farko da kuma yanzu, zuwa kafofin sada zumunta.


A sakamakon shigowar kafofin watsa labarai ta hanyar shafukan sada zumunta yanzu yasa labaran karya ya zama ruwan dare ta yadda sai an yi da gaske kafin a iya magance matsalar.


Kafin zuwan kafofin sada zumunta, kafofin watsa labarai irin su rediyo da jaridu ne aka fi dogara da su wajen samun labarai, amma yanzu kafar sadarwa ta sada zumunta ta mamaye harkar sadarwa ta yadda hatta kafafen watsa labarai ma suna amfani da wannan hanyar wajen samun labaran da za su yi amfani da su.

A shekarun baya wata ta watsa labarin cewa idan aka yi wanka da ruwan gishiri kuma aka sha za a tsira daga cutar Ebola. Daga baya aka gane cewa labarin karya ne, wata ce kawai ta kirkiri labarin da wasa ta tura wa wadansu a matsayin raha, amma labarin ya watsu nan da nan, daga bisani ya yi sanadiyyar tayar wa mutane masu hawan jini da ciwonsu, wadansu kuma suka rasa rayukansu. Illar yada labarin karya ke nan. Idan aka dauki wasu matakan, kowa zai iya hanga labaran karya daga nesa.


Wasu hanyoyi gane labaran karya

Kadda a karanta kanun kadai

Duba kwanan watan labarin

Duba marubucin labarin

Shin sauran Shafuka labarai na intanet suna rahoto a kan labarin?

Yiwuwar ita ce, idan galibin sauran rukunin yanar gizon suna ba da rahoto akan labari ɗaya, aƙalla gaskiya ne.

Karanta labarai da yawa akan batu guda don ganin menene tushen da ake amfani da su da kuma inda bambance-bambancen suke

Idan labarin yana da kuskuren kalmomi, kalmomi a cikin manyan haruffa, nahawu mara kyau, ko yawan amfani da “!!!!,”

Shin labarin yana da daidaitaccen rubutun kalmomi, nahawu, da rubutu?

Yi tunani kafin ka wallafa: Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani. Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu ya ke


Binciki asalin labarin: Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa. Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.


Duba wasu karin hanyoyin: Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu. Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?


Hanyoyin bincika labari: Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa. Tabbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.


✍️Mahadi Umar Imam

©Muryar Labarai 

Post a Comment

0 Comments