Yan bindiga sun Kara kashe wasu mutum biyu baya ga matashiyar nan Nabeeha Al-kadriyar, sannan Kuma sun kara yawan kuɗin fansa.

Yan bindiga sun Kara kashe wasu  mutum biyu baya ga matashiyar nan Nabeeha Al-kadriyar, sannan Kuma  sun kara yawan kuɗin fansa.




Ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda satar mutane ke ƙara yawaita a sassa daban-daban na Najeriya, musamman a baya-bayan nan.


Hakan dai na zuwa ne bayan samun rahotannin cewa ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da wasu mutane a yankin birnin Abuja sun kashe wasu ƙarin mutum biyu baya ga matashiyar nan Nabeeha Al-kadriyar, kana suka ƙara yawan kuɗin da suke neman a ba su kafin su sako sauran.


Wani masani kan harkokin tsaro Dakta Kabiru Adamu, ya shaida wa BBC cewa har yanzu matakan tsaron da ake ɗauka ba su wadatar ba saboda har yanzu ba a yi nasarar daƙile kafofin da 'yan bindiga ke amfani da su wajen karɓar kuɗaɗɗen fansa ba.


Ya ce har yanzu akan yi amfani da asusun ajiyar bankuna wurin karɓar kuɗin fansa kuma har yanzu jami'an tsaro ba su iya hana 'yan bindiga yin hakan ba.


 Idan muka yi misali da na baya-bayan nan na matashiyar nan da aka kame, muna da labarin cewa har yanzu suna tuntuɓar 'yan uwanta ta waya, an kwashe kwanaki ana haka. Kuma a ce wai har sun kashe ta sun mayar da gawarta, kuma dukkan jami'an tsaro ba su ɗauki mataki ba wurin kame su.' In ji shi


Ya yi bayanin cewa ba kasafai ya kamata a ce ana tattaunawa da waɗannan 'yan bindiga ba, saboda irin wannan shiga tsakani da ake yi domin a sami sulhu akwai iliminsa na musamman kuma ƙwararru ne kaɗai ya kamata a ce suna wannan aiki na shiga tsakani idan har ana fuskantar lamari irin wannan

Sakamakon sace mutanen da aka yi a yankin birnin Abuja har mutane sun shiga gangamin tara kuɗaɗe domin biyan kudin fansa, amma Dr Adamu ya ce wannan babban kuskure ne.


Ya ce: ' Yadda ake amfani da kafafen yaɗa labarai da makamantansu ana nuna cewa ana tara kuɗaɗe ba ƙaramin kuskure ba ne, don ya bai wa waɗannan 'yan bindiga damar ci gaba da cin karensu babu babbaka, saboda su ma suna kan waɗannan kafofi kuma suna ganin abin da ke faruwa.' A cewarsa


Ya ƙara da cewa, 'ba wai tara kuɗin ne ke da laifi ba, yadda aka tara kuɗin ne, kuma har wani wanda ake ganinsa da kima ya fito fili ya ce ya tara kuɗaɗe masu yawa, bai taimaka wa al'amarin ba ko kaɗan.


Dr Adamu ya ce akwai buƙatar a samu ƙwararru da za su tafiyar da al'amuran shiga tsakanin jama'a da 'yan bindiga domin a tabbatar da cewa an bi matakan da suka dace wurin biyan kuɗaden fansa domin tabbatar da cewa yin haka ba zai taimaka wa 'yan bindigar wurin ci gaba da gudanar da al'amuransu ba.

Post a Comment

0 Comments