Yan bindiga sun kashe Wani hakimi da wasu Karin mutum takwas ciki harda yayansa hudu a Katsina.

Yan bindiga sun kashe Wani hakimi da wasu Karin mutum takwas ciki harda yayansa hudu a Katsina.




 ‘Yan bindiga sun kashe Wani hakimi a Katsina da wasu Karin mutum takwas.


Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari da sanyin safiyar ranar Alhamis a kauyen Kuka Babangida da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, inda suka kashe mutane akalla tara ciki har da hakimin kauyen, da dandanshi Idris Haruna.


Shugaban karamar hukumar Bashir Sabiu ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, ASP Abubakar Aliyu. Jaridar Muryar Labarai ta samu tabbacin cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne ‘yan mintuna kadan kafin tsakar dare inda suka yi ta kai farmaki har zuwa karfe 1:30 na safiyar ranar Alhamis din.


Mazauna kauyen sun Shaidama wakilin Muryar Labarai cewa ‘yan fashin sun dauki lokaci suna bi gida-gida suna neman wasu abubuwa masu daraja da suka hada da kudi.


Majiyar ta kuma bayyana mana cewa ‘yan bindigar sun kashe hakimin kauyen, da ‘ya’yansa hudu, da kuma wasu hudu a cikin lamarin. Ba a iya tabbatar da ko sun sace mutane ko sun tafi da kayayyaki masu daraja.


Kwamishinan tsaro na jihar, Nasiru Muazu wanda ya bayyana hakan ta bakin mai magana da yawunsa Hassan Dan-Alli ya ce, “Jihar ta dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa jama’armu sun tsira a duk inda suke.”


®Muryar Labarai

Post a Comment

0 Comments