'Yan wasan Falasdinu na shirin buga Gasar cin kofin Asiya ta 2023 a yayin da Isra'ila ke kai hare-hare a Gaza.
‘Yan wasan suna cikin ''damuwa da fargaba kan halin da iyalansu ke ciki,”a cewar kocinsu, inda ya kara da cewa wasu daga cikinsu sun rasa ‘yan uwansu, sannan an lalata filayen wasa da mayar da wuraren wajen binne gawawwaki saboda rashin makabarta.
biyu gabanin wasan farko na Falasdinu a gasar cin kofin nahiyar Asiya na shekarar 2023 da za a yi a Qatar, kungiyar na fafutukar mayar da hankali ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza yaki a Zirin Gaza da aka yi wa kawanya, inda aka kashe dubban mutane tare da jikkata miliyoyi sakamakon mamayar Isra'ila a yankin.
Wasu daga cikin 'yan wasan sun rasa 'yan uwansu a hare-haren da Isra'ila ke kai wa yankin da aka yi wa kawanya bayan harin ba-zata da kungiyar gwagwarmayar Hamas ta kai a kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.
An lalata akasarin yankunan da ke Gaza, ciki har da filayen wasanni a hare-haren bama-bamai da bindigogi da Isra'ila ke kai wa ta sama da kuma mamayar kasa.
Filayen wasan kwallon kafa sun zama wuraren binne jama'a na wucin gadi sakamakon cikar da makabartu suka yi ko kuma rashin iya shiga wurin da za a binne gawa.
"Kowa na jin labaran abubuwan da ke faruwa, kafin da kuma bayan atisaye, a cikin motar bas ko kuma a otal,'' a cewar kocin kungiyar kwallon kafa ta Falasdinu, Makram Daboub daga kasar Saudiyya inda 'yan wasan ke atisaye.
Qatar ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Asiya ta shekarar 2023 daga ranar 12 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu, kuma Falasdinu za ta buga wasanta na farko a ranar 14 ga watan Janairu da Iran.
A ko da yaushe 'yan wasan na cikin "damuwa da fargaba kan halin da iyalai da 'yan'uwansu suke ciki", a cewar Daboub, tsohon kocin Tunisiya, ta wayar tarho.
A watan Yunin bara ne hukumar kwallon kafa ta Falasdinu ta yi bikin samun nasara - karo na uku - a gasar cin kofin nahiyar Asiya.
Sai dai ba tare da kawo karshen yakin da Isra'ila ke yi Gaza ba, a halin da ake ciki yanzu kungiyar ta shiga cikin zulumi a daidai lokacin da take kokarin tunkarar gasar da ke tafe.
"Muna fuskantar matsaloli na motsa jiki da na fasahohi da kuma dabarun wasanni saboda dakatar da gasar da aka yi, sannan akwai matsalar da ta shafi kwakwalwa," in ji cewar Daboub.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba aka dakatar da duk wasu wasanni na kwallon kafa a Gaza da aka yi wa kawanya da kuma Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
'Yan wasa da dama na cikin zulumi, irin su Mahmoud Wadi da Mohammed Saleh, wadanda iyalansu suka makale a Gaza inda aka lalata gidajensu, a cewar Daboub.
"Suna shan wahala," in ji shi.
Wasu kuma suna da dangi da suka tsere wa harin bama-bamai da Isra'ila ke kai wa arewacin yankin tare da neman mafaka a kudancin kasar, "inda yanayi ke da wahala", in ji shi.
Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce kashi 85 cikin 100 na al'ummar Gaza miliyan 2.4 ne suka rasa matsugunansu, sannan babu wani yanki mai al'umma da ke da tsaro, la'akari da hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa daga yankunan arewa zuwa kudu.
0 Comments