Yanzu-yanzu: Mun samu tabbacin Mutuwar Mutum 103 a yau Laraba, yayin da 141 kuma suka jikkata a birnin Kerman na kasar Iran.

 Mun samu tabbacin Mutuwar Mutum 103 a yau Laraba, yayin da 141 kuma suka jikkata a birnin Kerman na kasar Iran.



 Bayan wasu tagwayen fashe-fashe da suka faru a kusa da wurin da aka binne kwamandan sojan kasar Qasem Soleimani da kasar Amurka ta kashe shekara hudu da suka wuce.


A wani harin da jami’ai suka kira harin ta’addanci a cewar kafar yada labarai ta kasar. IRNA ta kara da cewa fashewar ta farko ta kasance mai nisan kafa 2,300 (mita 700) daga kabarin Soleimani, kuma na biyun ya kasance mai nisan mil 0.6 (kilomita 1) yayin da maziyarta suka ziyarci wurin domin Tunawa da Shahadarsa.


An kashe Soleimani ne sakamakon harin da Amurka ta kai ta sama da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya ba da umarnin a filin jirgin saman Bagadaza shekaru hudu da suka gabata a ranar Laraba.


Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin. 


Hotuna da bidiyoyin da aka wallafa a kafafen yada labaran gwamnatin Iran sun nuna dimbin jama'a da suka taru a yankin bayan fashewar bam din.


Muryar Labarai

Post a Comment

0 Comments