Zamu ci gaba da kai hare-hare Tekun Maliya har sai an kai wa Gaza kayan agaji — Houthi
Za a ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke da alaƙa da Isra'ila har sai agaji ya isa ga al'ummar Falasdinu a Gaza, in ji shugaban Houthi na Yemen Abdul Malik al Houthi a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin.
"Kasarmu za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta har sai abinci da magunguna sun isa ga al'ummar Gaza," in ji shi.
Shugaban kungiyar ya kara da cewa ta'azzarar hare-haren da Amurka da Birtaniya suka kai musu ba zai haifar da sakamako mai kyau ba kuma ba zai daƙile "nufinmu da azamarmu ba".
0 Comments